Bullar wani zazzabi ta hallaka mutane 165 a Dafur | Labarai | DW | 06.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bullar wani zazzabi ta hallaka mutane 165 a Dafur

Hukumar lafiya ta duniya ta bada sanarwar cewar an samu barkewar wani zazzafan zazzabin cizon sauro a yankin Dafur da ke Sudan.

A sanarwar da hukumar ta fitar dazun nan ta ce kimanin mutane dari da sittin da biyar ne su ka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da zazzabin.

Da ya ke wa manema labarai karin haske game da bullar cutar, babban jami'in hukumar ta lafiya ta duniya a Dafur din Anshu Banerjee ya ce baya ga wadanda su ka rasu, wasu kuma da yawansu ya kai dari bakwai da talatin da biyu sun kamu da cutar daga watan Satumbar zuwa yau.

Hukumomin kiwon lafiya a yankin dai sun ce bullar zazzabin na da nasaba da rashin yi wa al'ummar Dafur din rigakafin kamuwa da cutar.

Bullar zazzabin dai a wannan karon ita ce mafi muni tun cikin shekara ta 1990 kamar yadda alkaluman hukumar lafiya ta duniya su ka nuna.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar