Bukukuwan sallah na gudana lafiya a Najeriya | Siyasa | DW | 06.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukukuwan sallah na gudana lafiya a Najeriya

A Borno da Yobe da ma sauran jihohin shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, an yi sallah lami lafiya inda hukumomin suka baiwa jama’a damar yin zirga-zirga da ababen hawa yayin bukukuwan sabanin shekarun baya.

Saurari sauti 03:22

Yadda bikin sallah ke gudana a Borno da Yobe

Yawancin jamaar jihohin Borno da Yobe sun yi sallah cikin kwanciyar hankali da lumana bayan da aka sakar musu mara domin yin zirga-zirga da ababen hawa, wanda aka shafe shekaru baa yi amfani da su ba a bukukuwan Sallah.

Wannan mataki ya sa alummar jihohin sun gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki kamar yadda Habu Amma Bama wani da ke da zama a Maiduguri ya shaida wa DW ta wayar tarho.

Sallar ba ta yi wa 'yan gudun armashi ba

Nigeria Ramadan

An yi sallah lafiya a Borno da Yobe

Dubban wadanda suka tsere wa rikicin Boko Haram kuma aka tsugunar da su a sansanoni dabn- dabnm a jihohin suna gudanar da bukukuwan Sallah cikin kunci, inda suke kokawa dangane da karancin abinci da kuma Kuncin rayuwa.

A sauran jihohin shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, an gudanar da bikin Sallar lami lafiya, amm cikin tsaurara matakan tsaro na ko ta kwana.
Sannan matsi na tattalin arizkin kasa ya sa da dama ba su samun damar yin dinkin Sallah ko abincin Sallah ba.

Sauti da bidiyo akan labarin