Bukukuwan sake haɗewar Jamus | Labarai | DW | 03.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukukuwan sake haɗewar Jamus

Jamus ta biya kuɗin diya na yaƙin duniya

default

Wannan buki ya kuma yi kiciɓis ne da ranar da Jamus ta biya ragowar kuɗin diyya da aka bita tun bayan yaƙin duniya na biyu, wanda wata yarjejeniya da aka sanya hannu akanta a birnin Versailles na ƙasar Faransa a shekarar 1918 ta tanadi bayar da shi. Bayan haka ne kuma aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta daban a shekarar 1953 wadda ta bukaci Jamus da ta biya ƙarin ruwa akan kuɗin na diyya in har ta nemi ta sake haɗewa. A ranar 3 ga watan Oktoban 1990 Jamus ta biya ragowar dm miliyan 240 na kuɗin diyyar. A yanzu Jamus ta kammala biyan wannan kuɗi bayan shekaru 20 kuma shekaru 92 tun bayan yaƙin duniya na farko. A shekarar 1988 ne dai Jamus ta biya kuɗin diyya game da yaƙin duniya na biyu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal