Bukukuwan Kirsimeti da Ebola a Saliyo | Labarai | DW | 12.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukukuwan Kirsimeti da Ebola a Saliyo

Kasar Saliyo ta sanar da haramta duk wasu shagulgula da ake yi domin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara sakamakon annobar cutar Ebola mai saurin kisa da ta addabi kasar.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar ke nuni da cewa yawan wadanda suka mutu sakamakon annobar cutar ta Ebola a kasashen Guinea da Saliyo din da kuma Laberiya ya karu zuwa 6,583 daga cikin mutane 18,188 da suka kamu da cutar. Mahukuntan kasar ta Saliyo dai sun ce za su tura sojoji a yayin bukukuwan na Kirsimeti domin su sanya idanu su kuma tabbatar da ganin al'umma basu cakudu ba domin yin shagulgulan, musamman ma a yankunan da Ebolan ta fi kamari. Shugaban sashin kula da annobar ta Ebola Palo Conteh ya shaidawa manema labarai a Freetown babban birnin kasar cewa, za su tabbatar da ganin babu wanda ya fito waje domin yin bukukuwan Kirsimetin da kuma sabuwar shekara a fadin kasar baki daya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman