Bukukuwan karamar Sallah a Nijar | Siyasa | DW | 05.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukukuwan karamar Sallah a Nijar

Tun da maraicen ranar Litinin ce majalisar musuluncin kasar ta sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a garuruwa dabam-dabam, wanda ya kawo karshen azumin watan Ramadan.

A wannan Talatar ce aka gudanar da hawan idin karamar Sallah da ake kira Sallar Azumi a birnin Damagaram, inda dubban jama’a suka halarci filin idi.

Kazalika sauran jama'a a wasu garuruwa kamar birnin Yamai da Maradi da Gaya da makamantansu an gudanar da bukin Sallar lami lafiya.

Bayan wanan hutuba ce dai mai alfarma sultan na Damagaram Alhaji Abubakar Sanda ya yi kira ga al'ummar musulmi da su gudanar da rayuwa mai abun koyi ga sauran jama'a.

A can ma dai jahar Diffa mai fama da rikicin kungiyar Boko Haram rahotanni na cewar al’umma sun gudanar da hawan idin lami lafiya cikin tsauraran matakan tsaro.

Sauti da bidiyo akan labarin