1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: An kammala bukukuwan al'adu na Carnival

Abdoulaye Mamane Amadou MAM
March 5, 2019

Jamusawa sun yi bukukuwan shekara-shekara na Carnival a cikin yanayi na annashuwa da farin ciki, birnin Kwalan na daya daga cikin muhimman wuraren da bikin ya fi daukar hankali.

https://p.dw.com/p/3EUUx
Bildergalerie Karnevalszüge | Rosenmontag in Mainz
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Arnold

Bukukuwan na Carnival na da matukar muhimmanci a tarihin rayuwar Jamusawa na shekaru aru-aru, a bikin na nuna al'ada Jamusawa na yin shiga iri-iri tamkar dai yanayin tashe da kuma hawan salla da ake samu a kasar Hausa. Wani al'amari kuma da ke karawa shagalin armashi shi ne yadda masu jerin gwanon a cikin manyan motocin da aka yi kwalliya ke watso kayan kwalam da makulashe ga mutanen da ke tsaye suna kallo, da suka hadar da alawa iri-iri da biskit da sauran kayan zaki albarkacin wannan rana.

Jama'a da dama kama daga 'yan kallo da masu jerin gwanon bikin na bayyana farin ciki da ganin wannan lokaci wanda kuma kake iya gani a zahiri ta fuskokinsu, duk da ruwan saman da aka fuskanta a wasu wurare. Sai dai bikin na bana ya kuma samu halartar 'yan kasashen waje da dama da ke zaune a nan Jamus, saboda hakan sallar ba ta Jamusawa kadai ce ba ina a cikin murna da farinciki suka yi ta nuna gamsuwa da ganin wannan rana.