Bukin tunawa da harin Amirka a Japan | Labarai | DW | 15.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukin tunawa da harin Amirka a Japan

Kasar Japan na gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar cikar shekaru 71 da yin sarandar da ta kawo karshen yakin yankin Pacipic, na lokacin yakin duniya na biyu.

A ranar 15 ga watan Agustan shekara ta 1945 ne dai Amirka ta kai wasu tagwayen hare-haren nukiliya a biranen Hiroshima da Nagasaki na kasar ta Japan, sarkin kasar na wancan lokaci Hirohito ya fito ya yi jawabin mika wuya kasarsa a wannan yaki. Da ya ke jawabi a gurin taron tunawa da wannan rana, Sarki Akihito mai shekaru 82 a duniya wanda kuma da ne ga tsohon sarkin marigayi Hirohito, ya bayyana cewa yana takaici idan ya waiwayi tarihin abin da ya wakana a baya, inda ya ce yana fatan yaki irin wannan ba zai kara afkuwa a nan gaba ba. Mutane sama da miliya uku ne dai da suka hadar da sojoji da fararen hula a kasar ta Japan, suka rasa rayukansu a yayin yakin duniyar na biyu.