Bukin ranar tunawa da Naƙasassu a Duniya | Siyasa | DW | 03.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukin ranar tunawa da Naƙasassu a Duniya

Najeriya ce ƙasar da tafi sauran ƙasashen Afrika yawan Naƙasassu, domin a yanzu haka tana da miliyan 19 cikin daga cikin al'ummarta miliyan 160.

Majalisar Ɗunkin Duniya ta keɓe wannan rana ce domin martaba wa Naƙasassu dake tsakanin al'umma.

Wasu daga cikin dubban guragu da makafi tare da kutare wasu masu fama da nau'uka daban daban da suka shafi na naƙasa sun tofa albarkacin bakinsu dangane da mahimmancin wannan rana.

Mallam Muntari saleh dai shine kakakin ƙungiyar makafin jihohin arewa 19 da ke nuna takaici dangane da gazawar gwamnatin jihohi da na tarayyar Najeriya wajan kulawa da masu fama da naƙasa.

Ya ce " ya kamata su tattaru wuri ɗaya su fara gudanar da addu'o'i don samun taimako daga ubangiji, domin su kam sun gaji da ganin irin yaudarar da ake yi masu ta cewa za a ɓullo da hanyoyin tallafa masu. A cewar sa nakasasun Najeriya sune ke fuskantar ƙiyayya daga ɓangaren hukumomi.

A wata ƙiddigar da aka fitar a hukumance, an kiyasin cewa Najeriya ita ce ƙasar da tafi sauran kasashen Afrika yawan nakasassu,domin a yanzu haka tana da miliyan 19 chikin miliyan 160 na al'umman ƙasar.Bugu da kari a kullun ana samun ƙaruwar yawan jama'a dake samun nakasa walau ta sanadiyyar hatsarin mota, ko tashe tashen hankula na siyasa ko kuma rikicin kabilanci.

Hadiza umar ita ce dai shugaban mata kutare ta jihohin arewa wadda tace har yanzu dai basu gani a ƙasa ba, domin batun kulawa da naƙasassu da sauran dukkanin yaran da ke a faɗin Najeriya,wannan hakki ne da ya wajaba a kan gwamnatin tarayar Najeriya, matan kutare ba a kulawa da su ta dukkanin abubuwan more rayuwa da suke bukata, dan saboda haka lallai gwamnati na da gagarumar aiki akanta wajan kula da alummanta.

Naƙasassu na fuskantar koma baya a Najeriya

Nakasassu a Najeriya a kullun dai sai fuskantar koma baya suke yi, kama tun daga matsalar rashin makarantun yayan su, ya zuwa ga yadda suma kananan yaran ke tasowa da ayyukan barace barace.

Mallam Abdullahi Sama'ila na dai zamo sarkin guragun kaduna. Yace yakamata dukkanin manyan attajiran Najeriya su fara tallafa wa naƙasassu, domin halin da ake ciki na kulawa da 'ya'yan su na neman fin ƙarfin su, ya kara da cewa ƙananan yaran su na neman ilmi kamar kowane yaro a duniya, dan saboda haka akwai buƙatar daukar dukkanin kwararan matakan da suka chanchanta na bullo da hanyoyin cetar yayan marayu da nakasassu.

Idan dai ba a manta ba a shekarar data gabata ƙungiyoyin nakasasun Najeriya sun gudanar da zanga zanga da bore a jihohi daban daban na bukatar a samar masu tasu ma'aikatar da zata rika kulawa da su maimakon haɗa su da ma'aikatar dake kula da hakkokin mata.sun nunar da cewa akwai buƙatar 'yan majalisun jihohi su gaggauta sanya hannu ga dokar 'yancin naƙasassu a Najeriya.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin