Bukin al´adu na Karneval a tarayyar Jamus | Zamantakewa | DW | 17.02.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukin al´adu na Karneval a tarayyar Jamus

Tun a lokacin daular Romawa da Girikawa ake gudanar da bukin Karneval a sassa dabam-dabam na Jamus.

Bukin Karneval a Jamus

Bukin Karneval a Jamus

Jama´a masu sauraro bakrkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi al´adu, addinai da zamantakewa a sassa daban daban na duniya. Tun daga tsakiyar wannan mako bukin karneval ya kankama a wasu yankuna na tarayyar Jamus, inda jama´a ke gudanar da wannan buki. A bana dai bisa ga dukkan alamu an fara wannan buki ne wanda zai kai kololuwarsa a ranar litinin mai zuwa, tun bayan lashe gasar cin kofin kwallon hannu na duniya da Jamus ta yi a birnin Kolon, a farkon makon da ya gabata. To shirin na yau zai duba tarihin bukin na Karneval ne da kuma yadda ake gudanar da shi a nan Jamus. Masu sauraro MNA ke lale marhabin da saduwa da ku a wannan lokaci.

Musik.............Musik

Madalla: A nan Jamus kamar a sauran kasashen duniya, ko-wane yanki na kasar na da buki ko bukukuwan da ya ke yi a ko-wace shekara. Alal misali a yankin Rheinland, yankin da ya hade jihohin NRW da Rheinland-Palatinate, bikin Carnival ne ya fi daukar hankali kuma yake da muhimmanci ga al´ummonin wannan yanki. Kamar yadda sunan sa ke yin nuni, yankin na Rheinland ya hada garuruwa da birane da kogin Rhein ya ratsa a ciki. Daga cikin biranen kuwa akwai Kolon da Düsseldorf da Bonn a jihar NRW sai kuma Mainz a jihar Rheinland-Palatinate. Ban da wadannan biranen, akwai wasu garuruwa da kyauyuka da dama, to sai dai a wadannan biranen 4 bukin Carneval din ya fi yin armashi.

B: Bukin Carnival dai ya samo asali ne tun a zamanin daular Romawa da Girikawa. A wannan zamani dai Romawa da Girikawa na bukin fara lokacin zafi ne don girmama allolin su kamar Dionysos da kuma Saturn ta hanyar shan barasa da kade-kade da rera wakoki. Kamar dai Romawa da Girikawa, su ma jamusawan zamanin da na wannan bukin don girmamawa tare godewa allolin su, wadanda suka kori shedanai na lokacin sanyin hunturu. Amma daga baya, da tafiya ta yi tafiya sai mabiya addinin kirista suka karbi wannan al´ada ta bukin Carnival. To sai dai duk da karbar bukin Carnaval din da kiristoci suka yi, hukumomi da kuma majami´u sun ci-gaba da nuna rashin jin dadi ga yadda ake gudanar da bukin, musamman kayan da ake sanyawa da kuma wasu abubuwa da ba su kamata ba da ake yi a lokacin bukin. Duk da dokokin haramta wadannan halaye da munanan tabi´u a lokacin Carnival da hukuma ta kafa, bai sa an daina yin su ba, sai wasu ´yan kwarya-kwaryar canje-canje da aka samu.

A: A cikin karni na 18, bukin Carnival ya dauki wani sabon salo, inda masu buki ke sanya kayan ado da na rufe fuska irin na ´yan daular Venetia. Gabanin wannan lokaci, masu mulki da kuma masu hannu da shuni na wannan zamani kadai ke da ´yancin sanya irin wadannan kayayyaki. A cikin shekarar 1736, aka gudanar da bukin Carneval na farko na wannan sabon salon a tsakiyar birnin Kolon. Sannan shekaru 50 bayan haka, lokacin da dakarun juyin juya hali na kasar Faransa suka ci birnin Kolon da yaki, sun amince mazauna birnin su ci-gaba da gudanar da bukin tare da yin fareti akan tituna a lokutan Carnival. Ba´a jima da haka ba sai ´yan daular Prussia suka karbi jan ragamar mulki a birnin na Kolon. Ko da yake Prusiyawan sun fi Faransawan tsanani, amma hakan bai hana jama´ar wannan birni tafiyar da al´adar su kamar yadda suka saba ba.

B: Duk da kasancewa bukin Carnival na da dadadden tarihi, amma yadda ake gudanar da bikin ko kuma ake hawan Carneval din a yanzu, ya fara ne kimanin shekaru 178 da suka wuce. A cikin shekarar 1823 aka kafa kwamitin shiryawa tare da tafiyar da bukukuwan Carnival. Hakan ta karawa bukin armashi, abin da ya kai ga nada jarumin Carnival, amma yanzu aka sauya ya zama yariman Carnival. A ran 10 ga watan fabrairun 1823 jaruman Carnival suka fara yin hawa a lokacin bukuwan a birnin Kolon. Kafa wannan kwamiti ke da wuya, sai sauran birane da garuruwa, wadanda ma basa bakin kogin na Rhein kuma bisa al´ada ba sa gudanar da bukin Carnival su ma sun bi sahu, inda suka yi ta kakkafa kungiyoyi na Carnival. Har bayan karni na 19 an ci-gaba da kafa irin wadannan kungiyoyin ´yan hawan Carnival, kana a cikin shekara 1906 aka fara ba yariman Carnival dogarai.

A: A kowace shekara, kakar bukin Carneval kan fara ne a ran 11 ga watan 11 kana kuma bukin ya na kai kololuwar sa a wata ranar litinin da akewa lakabi da Litinin mai kyalli a cikin watan fabarairu, wato kakar kan dauki sama da watanni uku. A bana a ranar litinin 19 ga watannan na fabarairu bukin ke kai kololuwars, inda ake maci da jerin gwano akan titunan manyan birane da garuruwan da bukin ake bukin. Kakar bukin kan kawo karshe ne a ran larabar da ke biye da ranar litinin din, wato kwana daya kafin mabiya addinin kirista su fara azumin kwana 40 gabanin bikin ista.

C: Ga mata kuwa ranar da tafi muhimmanci a garesu a lokacin bukin Carneval, ita ce ranar alhamis, wato kwana 4 kafin a yi hawan Carneval din. A wannan rana mata na mamaye ofisoshin magadan gari tare da cin karensu babu babbaka akan tituna. A ranar hawan kuma, wato ranar da bukin ke kai kololuwarsa, jama´ar gari kan yi cincirindo akan tituna, inda masu bukin ke bi. Ana rarraba kyaututtuka kamar cakulan, alawa, furanni da dai sauransu ga ´yan kallo. A da dai wannan rana, ranar hutu ce a duk fadin yankin Rheinland, amma yanzu saboda dalilai na tattalin arziki, an soke hutun, amma duk da haka babu mai zuwa aiki a wannan rana a yankunan da ake gudanar da bukin. Kuma yanzu da yake hukuma ta zame hannunta, kamfanoni da masana´antu masu zaman kansu ne ke daukar nauyin gudanar da wannan buki na Carneval.

To DW na fata a sha shagulgulan Karneval lafiya.

 • Kwanan wata 17.02.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvT0
 • Kwanan wata 17.02.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvT0