Bukatar samun limamai cikin sojojin Jamus | Zamantakewa | DW | 28.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukatar samun limamai cikin sojojin Jamus

Sojoji Musulmi a Tarayyar Jamus, na ganin cewa rundunar tsaron kasar ta Bundeswehr ta manta da su, a wasu muhimman batutuwa da ya shafi rayuwarsu a yayin da suke wa kasar hidima a ketare.

Deutschland Bundewehr | Kommando Spezialkräfte KSK | Schleswig-Holstein (picture-alliance/dpa/C. Rehder)

Sojojin da suka kasance Musulmi na fusklantar kalubale a rundunar sojojin Jamus

A addinance dai, ba a kulawa da sojoji Musulmi da ke yi wa rundunar sojojin ta Bundeswehr hidima a ketare. Lieutenant Nariman Hammoubti-Rheinke ta jefa rayuwarta cikin hadarin aiki a rundunar Jamus da ke Afganistan. Sai dai a addinance ta na ganin, rundunar ta bar ta a baya. Jami'ar rundunar tsaron Jamus ta Bundeswehr din mai shekaru 41 da haihuwa, ta kan tuna irin hatsarin da mutum ya kan tsinci kanshi a ciki na tsawon kwanaki ko makonni kai har ma watanni, idan tana magana kan lokacin da ta yi aiki ga rundunar: "A kasar Afghanistan kullum kana cikin damuwa da fargaba. Za a iya harbe ka a sansani ko kuma a wajen sansanin. Na tsinci kaina cikin wani yanayi na tunani mai zurfi, yanayi ne mawuyaci. Ina wannan wuri na tsawon kwanaki uku. Ba wai batu ne na atisaye ko gwaji ba. Wannan harbi ne na ainihi, makaman rokoki ake harbo maka."

Nariman Hammouti-Reinke (Patrice Kunte)

Laftanar Nariman Hammouti-Reinke

Lieutenat Hammouni-Reinke musulma ce kuma Bajamushiya. Duk da cewar iyayenta 'yan asalin kasar Morocco ne, a birnin Hannover da ke arewacin Jamus aka haifeta. A gareta, shiriyata don tafiya yiwa kasarta aiki a ketare ya shafi rayuwarta da ma addininta. Kamar yadda jami'ar ta shaidawa tashar DW a hirar da aka yi da ita. "A wajena, tabbas hakan har yanzu nuna wariya ne da rashin daidaitawa. Domin wannan yana nufin cewa dole ne in kula da al'amurana da kaina da matsalolina, wajibi ne in tsara bayanan da zan bar wa shugabana, tare da tunanin wanda zai kai wa iyayena labarin mutuwata, idan har hakan ta kasance. Waɗannan kalilan ne kawai daga tarin batutuwan. Hakan ba adalci ba ne a gare ni, kuma a ganina tamkar har yanzu Musulunci bai iso Jamus ba, duk da cewar muna bautawa kasarmu kuma zamu iya sadaukar da rayukanmu saboda Jamus."

Berlin I Kramp-Karrenbauer stellt Dein Jahr für Deutschland vor (picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka)

Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer

A karshen watan Janairu dai ministar tsaro Annegret Kramp-Karrenbauer ta gana da shugaban majalisar Musulmi ta tarayya, Aimam Mayyek a wani taron da ya hada wakilan addinai a kasar, inda ministar ta yi magana dangane da magance wannan matsala, amma tun bayan wannan furucin har yanzu babu abin da ya sauya, duk da cewar a bainar 'yan jarida Karrenbauer ta yi wannan alkawarin. Bayan muhawara a matakan majalisa da 'yan siyasa dai, Kramp-Karrenbauer da shugaban Yahudawa na Jamus Joseph Schuster sun rattaba hannu kan sanya mai hidimar addinin Yahudawa a rundunar ketare a gaban shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier.

Alkaluman dai na bayanin kansu. A yanzu haka rundunar na da jami'ai dubu 185. Daga cikinsu akwai 'yan darikar Protestant dubu 53,400 dubu 41 mabiya darikar Katolika. Akawai Yahudawa 300 kana Musulmi 3,000 a rundunar ta Bundeswehr. Idan aka tura soja Musulmi zuwa wurin aiki mai hadari, to wajibi ne mutum ya tsarawa kansa komai, saboda babu wani malamin addinin Musulunci a cikin rundunar da zai yi wa gawarka hidima idan ta Allah ta kasance, ba kamar Kiristoci ba da kuma Yahudawa da su ma ake shirin ba su mai kula da su nan gaba kadan. Wannan wariya ce da nuna bambanci a fili karara.