Bukatar samun cikakken tsaro lokacin Kirsimeti | Zamantakewa | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukatar samun cikakken tsaro lokacin Kirsimeti

Shugabanin addinin kirista a jihar Filato sun bukaci samun cikkaken tsaro don bai wa mabiya damar gudunar da hidimomin Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tuni dai har hukumomin tsaron jihar suka amsa wannan kira na shugabanin, inda suka sheda wa manema labarai cewar sun kara karfafa tsaron mujami'u, da wuraren shakatawa da aka saba wasanni na bikin Kisimeti kana jami'an tsaron hadin guiwa sun kara daukan matakai na tsaro a fadin jihar Filato baki daya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Filato Nasiru Oki, cikin wata sanarwar da ya gabatar wa manema labarai a Jos, ya ce rundunar 'yan sanda ta haramta fasa shuw-bom, ko kuwa fashe fashen ababe masu kara, ko daukan hankali a lokacin bikin Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Kafin yanzu ma dai shugabannin addinan sun nuna damuwa ne musamam ma ganin yadda a kan samu fashe fashen boma-bomai a wuraren ibada a lokuta kamar haka, lamarin da shugaban Bishop Bishop na Katolika a Najeriya, kuma Archbishop na Jos Ignatius Kaigama ya ce abin damuwa ne matuka.

Baza jami'an tsaro wurare daban-daban

Wata majiya ta ce an tura jami'an soji da 'yan sanda da kuma jami'an Civil Defence wurare daban-daban don tabbatar da tsaro a wannan lokaci na Kirsimeti.

To sai dai Rev. James K Musa, babban sakataren Pastoci na Ilikiyas EYN, ya ce lokaci ya yi da talakawan Najeriya za su yi wa kansu fada game da duk wani rikici na addini.

A bangare guda kuma, babban jami'in gudanarwa na kungiyar Kiristocin Nageriya bangaren matasa, Injiniya Daniel Kazai, ya ce shugabannin matasa na Kirista za su yi anfani da damar bikin na Kirsimetti a bana wajen hada kawunan matasa a Najeriya-Musulmi da Kirista, don tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Sauti da bidiyo akan labarin