1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakon yadda za ta kaya a shirin kama al-Bashir

Yusuf BalaJune 15, 2015

Kamal Ismail, ministan kasa a ma'aikatar harkokin kasashen wajen Sudan ya ce wannan bukatar kotu ta a mika al-Bashir zuwa ICC ba zai yiwu ba.

https://p.dw.com/p/1FhEK
Südafrika Omar al-Baschir in Johannesburg
Shugaba Omar al-Bashir na SudanHoto: Reuters/S. Sibeko

Shugabannin kassahen Afrika na kammala taron kolinsu yayin da batun sammacen kama shugaba Omar al-Bashir, da kotun ICC ke nema ya dauki hankali a wajen taron AU bayan da wata kotu a kasar ta Afrika ta Kudu ta nemi kada ya fita daga kasar.

A cewar Kamal Ismail, ministan kasa a ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta Sudan, wannan bukatar kotu babu wani tasiri da za ta yi babu kuma wata baraza da shugaban nasu zai fuskanta za su koma gida lafiya.

Wasu lauyoyi ne dai suka gabatar da wannan bukata a kotu inda suka bukaci gwamnatin wannan kasa ta mika shugaba al-Bashir ga kotun ta ICC. Sai dai babu wasu alamun cewa gwamnatin na da niyyar mika shi bayan da ta bayyana shi a matsyin bakonta da ke halartar taron na AU.