1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar isar da agajin gagawa a Sudan

Binta Aliyu Zurmi
August 24, 2024

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka gami da wasu kasashe na shirin aikewa da abinci gami da magunguna zuwa sansanonin da al'ummar kasar Sudan ke tsugunne suna neman mafaka wadanda ke fama da matsananciyar yunwa.

https://p.dw.com/p/4jsFn
Sudan Darfur El Fasher
Hoto: AFP

A watan da ya gabata ne wasu kwararu na kasa da kasa suka yi gargadin cewa sama da rabin al'ummar Sudan miliyan 25.6 za su fada a matsanancin hali na yunwa musamman wadanda ke a manyan sansanonin da ke yankin Dafur, da tuni cutar kwalara ta barke a tsakaninsu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci masu yaki da juna a kasar da su bada damar shigar da maotoci dauke da kayayakin agaji ga mabukata cikin gagawa.

Wannan bayanin na kunshe ne a wata sanarwar da suka fidda a jiya Juma'a bayan kammala wani zama da ya gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland a kokarin kawo karshen rikicin da dakarun gwamnati da na rundunar sa kai ta RSF a Sudan din suka kwashe sama da watannin 16 suna gwabza kazamin fada.

A cewar masu shiga tsakanin wannan rikicin, kokarin sasanta bangarorin Sudan da ke gaba da juna ya ci tura.