1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar dakile samun kudin 'yan ta'adda

Muntaqa AhiwaFebruary 27, 2015

A yanzu haka dai kungiyoyin 'yan ta'adda sai karuwa suke yi a duniya, inda kuma suke sayan makamai masu tsadan gaske, wannan ya jawo mahawara kan hanyar samun kudin kungiyoyin

https://p.dw.com/p/1DkyM
Symbolbild Islamischer Staat
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wata cibiya da ke Paris kasar Faransa mai yaki da hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi, ta fidda sanawar cewa, duniya na bukatar aiki tukuru, domin dakile hanyar da kungiyar IS ke samun kudin ta. A rahoton da kungiyar ta fitar yau Jumama'a, ta bukaci gwamnatocin kasashe su bada himma don katse hanyoyin da kugiyoyin ke samun kudin shiga. Rahoton yace akasarin hanyyoyin da kungiyar ke samun kudi, sun hada da fasa bankuna, da kwasar ajiya da aka yi a rumbuna, da sayar da danyen mai, da kuma karban kudin fansa a mutanen da suke sacewa. A cewar wannan cibiyar, harin jiragen sama da Amirka ke kai wa 'yan IS da kuma faduwar fashin mai a kasuwannin duniya, sun yi mummunan lahani ga kungiyar.