Bukatar daina zubar da jini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 28.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar daina zubar da jini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan shiga tsakanin da Turai ke yi a rikicin Jamhuriya Afirka Tsakiya.

A wannan Talatar (28. 01. 2014) ce kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya nuna goyon bayansa ga matakin da Kungiyar Tarayar Turai ta dauka na tura dakaru zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a dai dai lokacin da kasashen duniya ke kokarin kawo karshen zubar da jinin da kasar ke fama dashi. Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi amannar cewar, akwai bukatar tura dakarun da yawansu ya kai dubu goma domin maido da bin doka da oda, kamar yanda jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa kwamitin sulhun.

Da murya guda ce dai, kwamitin mai kasashe mambobi 15 ya yi na'am da tura dakarun na Kungiyar Tarayyar Turai, tare da basu izinin daukar dukkan matakan da suka wajaba domin bada kariya ga fararen hula, wadanda suka fada cikin mawuyacin hali, tun kimanin watanni goma kenan da 'yan tawaye suka kifar da gwamnati.

A makon jiya ne Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da tura dakaru dubu shida zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin tallafawa dakarun Kungiyar Tarayyar Afirka 3,500 da kuma dakarun Faransa 1,600 da ke can, da nufin kawo karshen fito na fito a tsakanin kungiyoyin mayakan sa kai na Musulmi da na Kirista.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal