Buhari:Ba zan yi gaggawar nada ministoci ba | Siyasa | DW | 12.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Mutanen da na sani zan nada ministoci

Buhari:Ba zan yi gaggawar nada ministoci ba

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace ba zai yi gaggawar nada ministoci ba har sai ya san kowa a cikinsu.

A wasu kasashen dai akan kafa majalisar zartarwa cikin tsawon mako daya, wata ma nan take yayin kuma da ba kasafai akan wuce tsawon wata guda ba tare da sanin alkiblar sabuwar gwamnati ba. Sai dai kuma daga dukkan alamu tarihi na neman maimaita kansa inda aka rantsar da shugaban kasar kuma aka share tsawon makonni dai har Shidda babu amo na nadin ministocin.

Wasu kalaman shugaban majalisar dattawan Najeriyar Sanata Ahmed Lawal cewa shugaban kasar na iya mika wa majalisar sunayen ministocin ta haifar da sabon fata a tsakanin 'yan kasar da ke zaman jira har ma da kagara. To sai dai kuma wani taro tsakanin shugaban kasar da shugabannin majalisun tarrayar kasar guda biyu ya kare da sanyaya gwiwa. An dai kammala taron ba tare da mika  sunayen ministocin ba kamar yadda aka yi fata shugaban kasar zai yi.

Duk da jan kafa ta gwamnatin dai tuni shugaban kasar ya fito fili yace sai ya san kowa a cikin 'yan majalisar ministocin dake zaman mafi tasiri kuma jagora ga kokari na cigaban kasar. A baya dai kuma a cewar shugaban kasar an tilasta masa share shekaru uku da rabi tare  da bakin da bashi da cikakken fahimtar ko su wanene a cikin majalisar.

Dr Haruna Yarima masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Ahmadu Bello dake a Zariya yace shugaban yana da bukatar shawara dama taka tsantsan a sabon aikin samar da ministocin. Duk da cewar tun a watan mayu ya yi rantsuwar kama aiki sai a watan Nuwamban shekarar 2015 shugaba Buhari ya rantsar da majalisar ministoci a wa'adin mulkinsa na farko abin da 'yan kasar ke dangantawa da tafiyar hawainiya .

 

Sauti da bidiyo akan labarin