Buhari: Zaman lafiya zai samu a Niger Delta | Labarai | DW | 31.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari: Zaman lafiya zai samu a Niger Delta

Shugaba Buhari ya bayyana haka a sakon sabuwar shekara bayan da kai hare-hare kan bututun mai a yankin ya haifar da babban nakasu ta fuskar tattalin arziki a Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Niger Delta mai arzikin mai  a shekarar 2017. Shugaban ya bayyana haka ne a sakon barka da sabuwar shekara da ya gabatar a wannan rana ta Asabar.

Kai hare-hare dai kan bututun mai a yankin na Niger Delta ya haifar da babban nakasu ga kasar ta Najeriya musamman ta fannin abin da ke shigar mata da kudaden shiga ta fuskar man fetur, abin da kasar ke dogaro da shi, inda aka samu koma baya da ke zama mafi muni cikin shekaru 25 da wannnan kasa ta gani cikin hada-hadarta cikin mambobin Kungiyar OPEC da suka ga komabaya su ma saboda faduwar farashin hajarsu a kasuwannin duniya.

Tun a watan Nuwamba an ga koma bayan kai hare-hare na tsagerun yankin na Niger Delta mai arzikin mai da ke neman kari na abin da ake ba wa yankinsu da ke zama mai koma baya duk da fitar da albarkatu na kasa cikinsa a arzikin kasa. Hakan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da Shugaba Buhari ya yi da dattawa na yankin.