Buhari ya yi kira ga ′yan Najeriya su guji amfani da kalaman tsana | Labarai | DW | 25.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su guji amfani da kalaman tsana

Shugaba Buhari na Najeriya ya yi kiran 'yan kasar su guji amfani da kalaman da ka iya tayar da husuma a kasa.

A wani abn da ke zaman alamun sauki ga shugaban Tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari da yanzu haka ke jiyya a cikin birnin London na kasar Biratiya, a karon farko shugaban ya nemi 'yan kasar da su kau da maganganun tsana a tsakaninsu da nufin hada komai domin ciyar da kasar zuwa gaba.

A wani sakon Sallar da ya aike ga 'yan kasar, Buharin yayi godiya ga addu'o'i na 'yan kasar tare kuma da fatan sauke alkawura da gwamnatinsa ta dauka can baya.

Wannan ne dai karo na farko da al'ummar Najeriya ke ji daga shugaban da ya sa kafa ya bar kasar zuwa birnin London da nufin jiyya fiye da wata daya da rabi.

A baya dai an yi ta rade-radin lalacewa ta lafiyar kafin sabon sakon da ke iya kaiwa ga kwantar da hankula tsakanin al'ummar Najeriya.