1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya yi jawabi ga 'yan kasa

October 22, 2020

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi matasa masu zanga-zanga da su kauracewa tituna, saboda samun kafar tattaunawa da gwamnati domin kawo karshen tashe-tashen hankula a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/3kJ7j
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

A cikin wani jawabi na mintuna Tara da shugaban ya gabatar ga 'yan kasar, yace gwamnati ba za ta lamunci matakin da zai yi wa dimukuradiyya barazana ba. Shugaba Buhari ya umarci jami'an tsaro da su bi doka da oda yayin da bada kariya ga rayuka da kaddarorin al'umma, ya kuma bukaci kungiyoyi da kasashen duniya su zurfafa bincike kafin yanke hukuncin da babu gaskiya balle adalci a cikinsa.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da mutunta hakkin kowa a kasar ba tare da kyale tada hankalin al'umma 'yan kasa ba. Shugaban kasar ya kuma jero shirye shiryen gwamnati da matasa ke iya cin gajiyarsu da zai inganta rayuwar al'ummar kasa baki daya.