Buhari ya sa hannu kan dokar samar da ayyuka | Labarai | DW | 06.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya sa hannu kan dokar samar da ayyuka

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya amince da wani matakin da ake ganin zai zaburar da kamfanonin cikin gida don samar da ayyukan yi ga dumbin 'yan kasar da ke wadrin rashin abin yi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan wata dokar da ke umurnin amfani da kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida, a wani matakin gwamnati na kirkiro da ayyukan yi ga miliyoyin masu wadari babu ayyukan dogaro a kasar. Dama dai shugaban na Najeriya ya sha nanata aniyar ganin kasar ta rage dogaron da take yi kan man albarkatun man fetur da manufar samar da ayyukan a Najeriyar.

Dokar da sanya wa hannu, ta kuma haramta wa ma'aikatar harkokin cikin gida bada takardar izinin shiga kasar wato Visa, ga duk wasu ma'aikata ko kamfanonin da ba a gaza yin irin ayyukan da suke yi a kasar ba.

Cikin watan Mayun shekarar 2015, lokacin da shugaban ya kama mulki, babban bankin Najeriyar CBN ya takaita samar da kudaden kasashen waje ga masu shigar da hajoji daga ketare, duk dai a mataki na zaburar da masana'antun cikin gida don samar da ayyukan.