Buhari ya mika wa majalisa sunayen ministoci | BATUTUWA | DW | 23.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Buhari ya mika wa majalisa sunayen ministoci

Bayan share tsawon lokaci ana jira jin sunayen ministoci, Shugaba Buhari ya fitar da jerin sababin ministocin da yake son su ja ragamar kasar cikin mataki na gaba

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dokokin kasar sunayen mutanen da ya ke son yin aiki da su a matsayin ministoci domin majalisar ta tantancesu. Shugaban majalisar dattawan kasar Ahmad Lawan, ya karanta sunayen mutanen a zauren majalisar ga 'yan majalisar. Yawan mutanen dai ya kai 43 sabanin 36 da ya mika a zangon mulkinsa na farko.

Daga cikin sunayen da aka mika akwai wadanda ya yi aiki da su a baya ciki kuwa har da Rotimi Ameachi da Babatunde Fashola da Zainab Ahmad da kuma Lai Muhammad. Sabbin fuskoki a jerin sunayen kuwa sun hada da Dakta Isa Ali Pantami da Sabo Nanono da Pauline Tallen.Nan gaba ne dai majalisar dattawan za a yi wani zama na musamman domin tantance ministocin kafin daga bisani ta mika sunayen da ta amince da su ga shugaban kasar don rarraba musu ma'aikatu tare da rantsar da su.

Akalla ministoci 14 ne dai suke shirin dawo wa a cikin sabuwar majalisar da ke zaman irinta mafi tsawo cikin sama da shekaru 15 a kasar, ciki akwai mata guda Shida a cikin majalisar mai wakilai 43, a yayin kuma da jihohin Kano da Kaduna suka tashi da ministoci  bibbiyu. A ranar Laraba  mai zuwa, ake sa ran fara aikin tantance ministocin a majalisar dattawa ta kasar kafin daga baya akai ga rantsar dasu domin kamun aiki cikin matakin na gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin