Buhari ya lashe zaben Najeriya amma Atiku ya ce zai shigar da kara | Zamantakewa | DW | 28.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Buhari ya lashe zaben Najeriya amma Atiku ya ce zai shigar da kara

Jam’yyar PDP ta adawa ta ce ta yi watsi da sakamakon da aka bayana na shugaban kasa wanda Muhammadu Buhar ya samu nasara saboda ta ce babbu sahihanci a cikinsa.

A Najeriya, dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, ya ce zai shigar da kara gaban kotu don kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC nasara a babban zaben kasar da aka gudanar a makon jiya. Atikun dai ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira. A daya bangaren kuwa, Shugaba Buhari, a yayin jawabinsa na farko bayan lashe zaben, ya godewa dinbin al'ummar kasar da suka zabeshi da kuma amanar da suka ba shi kan ya ci gaba da jagorantarsu.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin