1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya gana da wasu gwamnoni a London

Gazali Abdou Tasawa
July 24, 2017

A karo na farko tun bayan da ya tafi jinya a birnin London yau sama da watannin biyu da rabi, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya mai shekaru 74 ya bayyana a bainar jama'a.

https://p.dw.com/p/2h2DT
Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

A karon farko tun bayan da ya tafi jinya a birnin London yau sama da watannin biyu da rabi, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya mai shekaru 74 ya bayyana a bainar jama'a.

A wani hoto da fadar shugaban na Najeriya ta wallafa a jiya Lahadi a shafinta na Twitter ta nuna shugaban kewayen wani teburi tare da rukunin wasu mutane wadanda fadar shugaban kasar ta ce ayarin gwamnanoni da shugabannin jam'iyyar  APC mai mulki ne a lokacin ganwar da suka yi da shugaban a jiya Lahadin.

 A sakon Twiiter fadar shugaban Najeriyar ta bayyana cewa shugaba Buhari na isar da gaisuwarsa ga 'yan Najeriya, kuma zai koma gida da zarar likitocinsa sun bashi izini. 

A cikin wata sanarwa da ya fitar daga nashi bangare wacce kuma fadar shugaban kasar ta wallafa a dai ranar ta lahadi, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha daya daga cikin mambobin ayarin mutanen da suka gana da Shugaban, ya ce sun kwashe sama da awa daya suna hira da shi a lokacin cin abincin rana, kuma a hirar tasu sun fahimci yana da masaniya kan duk abubuwan da ke wakana a kasar.