Buhari ya bata rai a kan almajiran Daura | Labarai | DW | 15.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya bata rai a kan almajiran Daura

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin rufe makarantar Islamiyar nan da aka gano yara a cikin wani mumunan hali a mazabarsa ta Daura a jihar Katsina, inda ya nuna bacin ransa.

Shugaba Buhari ya ce jami'an 'yan sanda su tarwatsa ire-iren wadannan gidajen da aka tsugunar da kangararrun yara.  A cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar a wannan Talata, ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da irin wadannan wuraren da ake cin zarafin mata da maza ba da sunan addini.

Mutune kusan saba'in aka 'yanto daga wata makarantar Islamiyya da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya, inda 'yan sanda suka kai samame tare da nasarar kubutar da mutanen masu shekaru tsakanin bakwai zuwa arba'in. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina Sanusi Buba ya ce bayan bincike da suka gudanar, daga cikin yaran sun fada musu yadda ake gallaza musu azaba.

Wannan samamen na jihar Katsina na zuwa ne kwanaki bayan wani da aka kai a jihar Kaduna, inda nan ma aka gano yaran da aka kai makarantar Islamiyyar da sunan karatu ,amma suka tsinci kansu cikin yanayi na kunci a sakamakon azabar da malamai ke gana musu.