Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa na ganin yadda wasu tsiraru suka danne tattalin arzikin kasar na lokaci mai nisa.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wajen taro na 25 da ake yi a Abuja, mai taken wanne hali Najeriya za ta samu kai a ciki a shekarar 2050. An dai shirya taron ne da nufin lalubo hanyoyin da za’a bi wajen magance abubuwan da ke hana tattalin arzikin kasar bunkasa. Sakamakon abin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke cewa tattalin arzikin kasar na hannun wasu tsirarun ‘yan kasar kawai. Masana tattalin arziki daga ciki da wajen Najeriyar ne dai suka halarci taron, inda wasu suka bayyana dalilan da ya sa tattalin arzikin ke tafiyar hawainiya. A cewar wani masanin tattalin arziki Yushau Aliyu tsarin siyasa na daga cikin abin da ke hana tattalin arzikin bunkuasa, baya ga cin hanci da rashawa.