1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari na ziyarar aiki a Afirka ta Kudu

Zulaiha Abubakar
October 3, 2019

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai gana da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa don tattauna harkokin kasuwanci da siyasa a lokacin da kasashen ke aikin farfado da tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3Qg8Q
Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Ziyarar Muhammadu Buhari ta kwanaki uku ta zo ne bayan da rikicin kyamar baki da ya sanya da dama daga cikn al'ummar Najeriya mazauna Afirka ta Kudu sun koma gida, ko da yake fadar mulkin kasar Afirka ta Kudu ba ta bayyana batun kyamar bakin daga cikin batutuwan da shugabannin biyu za su tabo ba. 

Sai dai sshugabannin za su jagoranci wani taron kara wa juna sani da wasu 'yan kasuwa suka shirya don magance baraka tsakanin kasashen biyu.