Buhari na son Tinubu ya kara wa ma'aikata albashi | Labarai | DW | 29.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari na son Tinubu ya kara wa ma'aikata albashi

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado a Najeriya ta bai wa zababben shugaban kasar Bola Tinubu shawarar kara wa ma'aikata albashi saboda shirin gwamnati na janye tallafin man fetur a watan Yuni mai zuwa.

Ministan kwadago na kasar Chris Ngige ne ya sanar da haka a ranar Talata, inda ya ce tuni dama gwamnati mai barin gado ta kammala shirya yadda za ta kara wa ma'aikata albashi domin rage radadin janye tallafin man fetur din.

Sai dai duk da cewa bai zama wajibi gwamnatin Tinubu ta yi aiki da wannan shawara ba, amma matakin ya kara dora mata matsin lamba kan cika alkawarin yakin neman zaben da Tinubu ya yi cewa zai janye tallafin man fetur — duk kuwa da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza janye shi saboda adawar da 'yan kasa ke nunawa.

Tun da farko dai zababben shugaba Tinubu ya sha alwashin karkatar da kudaden tallafin man fetur din zuwa ga ayyukan bunkasa walwalar 'yan kasa da gyaran tititunan da suka lalace gami da inganta ilimi da kiwon lafiya, amma bai ayyana batun karin albashi ba kamar yadda gwamnatin Buhari yanzu ke bayar da shawara.