1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari na son kawar da kwararar 'yan cirani

Ahmed SalisuFebruary 3, 2016

Shugaban Najeriya ya bayyana wa 'yan majalisar Turai cewar gwamnatinsa za ta hada kai da Kungiyar Tarayyar Turai wajen kawo karshen kwararar 'yan cirani daga Afirka.

https://p.dw.com/p/1HpGY
Straßburg Europäisches Parlament - Nigerias Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/V. Kessler

Shugaban na Najeriya Muhammdu Buhari ya ambata hakan ne a wannan Larabar yayin wani jawabi da ya yi gaban 'yan majalisar dokokin na Turai a zauren majalisarsu da ke birnin Starsbourg na kasar Faransa.

Yayin jawabin nasa, shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa za ta yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin ta bada gudumawarta da nufin dakile kwararar 'yan cirani daga Afirka zuwa Turai musamman ta tekun Bahar Rum inda da dama daga cikinsu kan rasa rayukansu a yunkurinsu na shiga Turai din inda ya kara da cewar:

"Gwamnatin Najeriya na aiki tukuru wajen magance abubuwan da ke sanya mutane kaura musamman ma daga Najeriya. A kasafin kudin wannan shekarar mun sanya batu na baiwa matasa kimanin dubu 500 aikin yi a makarantunmu. Muna kuma aiki tare da jihohi da kananan hukumomi don karfafa cibiyoyi na koyon sana'o'i don baiwa matasa horo don ya kasance sun zamto masu dogaro da kansu."

Nigeria Symbolbild Muhammadu Buhari Anti-Korruptions-Offensive
Buhari na son ganin an kawar da kalubalen tsaro a AfirkaHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

Tsaro ma dai musamman a nahiyar Afirka na daga cikin batutuwan da shugaban na Najeriya ya tabo a jawabin nasa, inda ya ke cewar dole ne a tashi tsaye wajen ganin an yi abinda ya kamata game da halin da kudancin Libiya ke ciki domin a rikicin da ke ruruwa a wajen ya sanya Sahel kasancewa kan wani bam da zai iya fashewa kowanne lokaci.

"Kudanci Libiya ya kasance wata kasuwa ta baje koli ta makamai da ke habaka wadda ke barazana ga tsaro a yankin Sahel da yammacin Afirka da ma abinda ya sha gaban haka. Don haka dole ne mu kara jan damara wajen daukar matakai da za su kawo karshen rikicin kasar Libiya."

Dangane da batun nan na 'yan matan Chibok kuwa, shugaban ya ce gwamnatinsa ba za ta gajiya ba har sai ta ga an kubuto da su kamar yadda ya yi wa iyayen yaran da 'yan Najeriya alkawari. Wannan ne ma ya sanya 'yan majalisar ta Turai da ya ke yi wa jawabin suka barke da tafi bayan da ya ambaci hakan.

To baya ga batu na kubuto da 'yan matan na Chibok, Buharin har wa yau ya shaidawa 'yan majalisar na Turai cewar gwamnatinsa na fadi-tashi wajen ganin ta kawo karshe rikicin Boko Haram baki daya don har ma sun sake fasalta tsarin rundunar sojin kasar kuma yanzu haka suna son ganin an sake gina yankin arewa maso gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya kassara.

Nigeria Boko Haram
Buhari ya sabunta alkawarinsa na ceto 'yan matan ChibokHoto: picture alliance/AP Photo

"Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen sake gina makarantu da asibitoci da sauran ababan more rayuwa da ke da muhimmacin gaske ga jama'a wanda 'yan ta'adda suka lalata kuma. zance da ake yi yanzu ma dai 'yan ta'addar sun takaita ne ga dajin Sambisa ko da dai su kan kai hare-hare nan da can amma ba su da karfin kame yanki ko wata gunduma."

Batutuwa da suka danganci bunkasa tattalin arzikin Najeriya da rage dogaro da mai da magance sace danyen mai da wasu ake yi da batun nan na yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin abubuwan da shugaban na Najeriya ya tabo, kan haka ne ma ya nemi tallafin Turai domin kaiwa ga cimma wannan nasarori.