Buhari na kan hanyarsa ta komawa Najeriya | Labarai | DW | 19.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari na kan hanyarsa ta komawa Najeriya

Fadar shugaban Najeriya da ke Abuja ta sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari na hanyarsa ta komawa gida bayan jiyyar da ya yi a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma gida a wannan Asabar, bayan daukar sama da watanni uku yana jiyya a birnin Landan na kasar Birtaniya. Wata sanarwar da ta fito daga fadar shugaba Buharin da ke Abuja, ta tabbatar da cewa shugaban zai koma Najeriya bayan gamsuwar da aka yi da saukin jikinsa.

Haka ma jagoran na Najeriya zai yi wa 'yan kasa jawabi a ranar Litinin da ke tafe, kamar yadda Femi Adesina, mai magana da yawun Buhari ya fada.

Tun a ranar 7 ga watan Mayun bana ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari, yake birnin na Landan don jiyyar larurar da mahukuntan kasar ba su fayyace ta ba.