Buhari: Muna jinjina wa China kan tallafi | Labarai | DW | 12.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari: Muna jinjina wa China kan tallafi

Shugaban kasar China Xi Jinping ya tabbatar wa tarayyar Najeriya hadin kan kasarsa a bangarorin masu tarin yawa, a yayin da ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

Xi Jinping ya ce shekara ta 2016 na kasancewa shekaru 45 cif da kulla dangantakar diplomasiya tsakanin China da Najeriya, kuma dukkanin kasashen sun ribaci dangantaka mai gwabi a tsakaninsu a bangarori da dama.

Kazalika Shugaban kasar China ya ce a shirye suke su kara kulla danganta da Najeriya a fannonin Ayyukan noma, kifi, matatun man fetur,da ma'adanan karkashin kasa gami da bunkasa harkokin masana'antu. 

Ana sa bangaren Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa China a bisa irin tallafin da kasar take baiwa Najeriya wajen habaka harkokin ci gaba.

Dukkanin shugabanin biyu sun rattaba hannu a kan wasu yarjeniyoyi masu dama ciki har da noma da sanya hannayen jari.