1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufar gwamnatin Buhari a wa'adin mulki na biyu

Abdullahi Tanko Bala
July 24, 2019

Gwamnatin tarrayar Najeriya da jihohin kasar game da masu takama da kasuwa dama kwarraru a sha'anin mulki sun ce sun kudiri aniyar samo hanyar cika alkawuran gwamnatocin bayan zabe.

https://p.dw.com/p/3Mg2y
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Ya zuwa yanzu dai yawan mutane a cikin Najeriya yana karuwa da tsakanin kaso 2.6 zuwa kaso Uku  a shekara a wani abun da ya maidata kan gaba ga karuwar al’umma a duniya baki daya. To sai dai fatara da talauci suna karuwa sakamakon tattalin arziki mara karfi da kuma dogaro da gwamnati a tsakanin al’umma. Abun kuma da ya dauki hankalin jam’iyyar APC mai mulki da ta shirya wani taro na daukacin zabbabunta da nufin nazarin sabbabin dabarun cika alkawarin da ta dauka yayin zabe.

Kokarin dorawa zuwa mataki na gaba, ko kuma mafarki a cikin neman cigaba na zaman komawa gona a tsakanin al’umma ta kasar. A fadar Atiku Bagudu dake zaman gwamnan Kebbi kuma mataimakin shugaban hukumar wadatar da kasa da abinci, kasar na kallon kwakkwarar cigaba daga irin nasarar da ake samu a harkar noman a yanzu.

A cikin wannan mako ne dai babban bankin kasar yace yana shirin hana bada kudin kasashe na waje da nufin sayo madarar shanu. Abun kuma dake neman kara karfi na sana’ar kiwo a jihohin arewacin kasar, a fadar Abdullahi Umar ganduje dake zaman gwamnan jihar Kano.

Akwai dai fatan cewa sabbabin dabarun na iya kara habbaka tattalin arziki dama kai karshen matsalar rashin tsaron a kasar a tunanin Mallam Bashir Ibrahim dake zaman wani mai sana’ar noma da kiwo a jihar Kano.

Abun jira a gani dai na zaman  tasirin sabbin dabarun a kokarin kai karshen fatara da talauci.