Buhari bai saba wa dokar kasa ba | Labarai | DW | 09.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari bai saba wa dokar kasa ba

Majalisar dattawan Najeriya ta ce babu wata dokar da ta hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zama don jinya a ketare sama da watanni uku.

Majalisar wadda ta sanar da hakan a zamanta na ranar Talata, ta ja hankalin wadanda suka shirya tare da halartar gangamin kiran shugaban ya dawo ko ya ajiye aiki, da cewa su kyale shugaba Buhari saboda babu wata dokar kasa da ya taka. Ta yi tur da boren, tare da yin kira ga wadanda suka tsara shi da cewa su nisanci ruruta rigimar siyasa ba tare da hujjoji masu gama jiki ba.

Tsarin mulkin Najeriya dai ya bayyana yadda shugaba ya kamata ya yi a lokuta makamantan wannan, inda ya ce shugaba ya mika ragama ga mataimakinsa ya kuma sanar da majalisun kasar batun tafiya jinyar, wanda kuwa majalisar ta ce an yi hakan. Batun rashin lafiyar shugaba Buhari dai na daukar hankali a ciki da ma wajen Najeriyar.