Buƙatar tura dakarun Afirka zuwa Mali | Labarai | DW | 28.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buƙatar tura dakarun Afirka zuwa Mali

Chadi ta buƙaci da a hanzarta tura dakarun Afirka zuwa Mali domin tinganta matakan tsaro a yankin arewacin Mali

Shugaban ƙasar Chadi Idriss Derby ya yi kira da a hanzarta tura dakarun Afirka zuwa Mali, lokacin wani taron wuni biyu na shugabannin yammacin Afirka, wanda aka fara ran laraba a Côte d'Ivoire, wanda kuma ke mayar da hankali kan matsalolin tsaro da ta'addancin da suka addabi yankin.

Duk da cewa a hukumance Chadi bata cikin ƙasashe 15 da ke ƙarƙashin laimar ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, ta tura dakarunta 2000 su taimaka ma dakarun da ke ƙarƙashin jagorancin Faransa waɗanda suke shiga mako na bakwai yanzu a aikin zakulo 'yan tawayen da suka addabi arewacin Mali.

Ƙudurin rundunar Africa da wasu ƙasashe a Mali ya yi kira da a tura dakaru dubu takwas a maimakon dubu uku da ɗari bakwan da aka sa tun farko wanda zata ƙunshi reshen 'yan sanda da fararen hula.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar