1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buɗaɗɗiyar wasiƙar Abzinawa zuwa ga shugaban Niger

February 8, 2013

Matsayin Abzinawa a Niger yana haddasa saɓani tsakaninsu da shugaban ƙasa, Mahamadou Issoufou

https://p.dw.com/p/17bDJ
Hoto: picture alliance/dpa

A jamhuriyar Niger tsohuwar kungiyar yan tawayen Abzinawa na kasar ce ta rubuta wata budaddiyar wasika zuwa ga shugaban kasar domin nuna rashin amincewarta a game da matsayin da shugaban kasar Ahaji Mahamadu Isufu da gomnatinsa su ke dauka a cikin rikicin kasar Mali, musamman dangane da batun da ya shafi kungiyar yan tawayen 'yan uwansu Abzinawan Malin ta MNLA, a wata fira da wasu kafofin yada labarai na Faransa a farkon wanann mako. A wata fira ta musamman da ya yi da gidan radion DW kakakin tsohuwar kungiyar yan tawayen Abzinawan kasar Niger ta MNJ, Mallam Seidu Kausen Maiga ya yiwa wakilimmu a yamai Gazali Abdou Tasawa karin bayani a game da dalillan rubutawa shugaban kasar wanann wasika, dama batutuwan da wasikar ta kunsa.

Wannan budaddiyar wasika wacce kakakin tsohuwar kungiyar yan tawayen Abzinawan kasar ta Niger ya rubuta ya kuma aikawa shugaban kasa ta biyo bayan wasu kalammai ne da shugaban kasar ta nigrer Alhaji Mahamadu Isufu ya furta a wat fira da ya yi da wasu kafofin yada labarai na kasar Faransa dangane da wasu batutuwa da su ka shafi makomar kungiyar yan tawayen Abzinawan kasar malin ta MNLA a cikin shirin sasanta yan kasar Malin da kasashen duniya ke son yi a nan gaba bayan korar kungiyoyin da ake kira na yan taadda daga yankin arewacin kasar Malin.

Daya daga cikin batutuwan da kakakin tsohuwar kungiyar yan tawayen abzinawan kasar niger din Mallam Seidu Kausen Maiga ya nuna rashin amincewarsa da shi shine zargin da shugaban kasar Niger din ya yi na cewa yan tawayen kungiyar MNLA sune ummulhabaisan matsalar da mali ta ke ciki a yau.

Niger Tuareg Friedensforum
Taron sulhu da yan kabilar AbzinawaHoto: Bettina Rühl

Haka zalika kakakin tsohuwar kungiyar ta MNJ ya ce ba su aminceba da bukatar da shugaban kasar niger ya nuna ta ganin an koncewa mayakan kungiyar MNLA damararsu a halin da ake cikinsa a yau a kasar Mali. A firar tasa da kafofin yada labaran kasar ta Faransa shugaban kasar ya bayyana cewa kungiyar MNLA ba ta cancanci wakiltar kabilar Abzinawan kasar Malin ba a cikin shirin sasantawa da za a yi tsakanin yan malin;akan wanann batuma dai kkk tsohuwar kungiyar yan tawayen abzinawan kasar niger din na da sabanin raayi.

Kakakin tsohuwar kungiyar yan tawayen Abzinawan kasar ta niger ya ci gaba da cewa ya san shugaban kasar niger na da fargabar abzinwan Niger suma su nemi yancin kasarsu kamar na mali a niger;akan wanann ya ce yan niger su kontar da hankalinsu ba su da irin wanann manufa. Amma dai daga karshe Mallam Seidu Kaousen Maiga ya ja hankalin shugabannnin kasar niger kan wata matsala da ya ke ganin in ba amaganceta ba na iya jefa niger din a irin halin da mali a tsinci kanta a cikinsa a yau.Yau dai kwanaki hudu kenan da kakakin tsohuwar kungiyar yan tawayen Abzinawan ya aikawa shugaban kasar ta Niger da wannan budaddiyar wasika sai dai har ya zuwa yau fadar shugaban kasar a ta ce uffan ba kan batun.