1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

British Airways zai biya diyya saboda mazambata

Yusuf Bala Nayaya
September 7, 2018

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya bayyana cewa zai biya diyya ga masu hulda da kamfanin wadanda aka sace bayanan katinansu na banki ta hanyar satar gwanayen iya sata a shafukan Intanet.

https://p.dw.com/p/34VPG
Großbritannien British Airways Perosnal protestiert vor dem Sitz der Qatar Airways in London
Hoto: Reuters/N. Hall

Shugaban hukumar gudanarwar kamfanin Alex Cruz ya bayyana batun biyan diyyar a wannan rana ta Juma'a lokacin da yake neman afuwar kamfanin ga masu hulda da kamfanin saboda matsalar da aka samu.

A yammacin Alhamis kamfanin jiragen saman na British Airways ya bayyana cewa bayanai da harkokin kudade na masu hulda da kamfanin su 380,000 da suka sayi tikiti ta hanyar shafin Intanet ko manhajar kamfanin tun daga ranar 21 ga watan Agusta zuwa ranar Laraba an sace su.

Wannan dai na zuwa ne watanni bayan da Kungiyar Tarayyar Turai ta tsaurara dokoki na kare bayanan al'umma karkashin dokar kare bayanai ta (GDPR).