Hadarin jirgin ruwa ya rutsa da bakin haure
December 14, 2022Firaiministan Britaniya Rishi Sunak, ya baiyana bakin cikinsa a gaban majalisar kasar, kan asarar rayuka da aka samu a sakamakon wani hadarin jirgin ruwa da ya rutsa da wasu bakin haure.
Da asubahin wannan Laraba, aka ja hankalin jami'an da ke aikin tsaron gabar ruwan kasar da ta hade Britaniya da Faransa kan hadarin da karamin kwale-kwalen da ya debo wasu bakin haure ya yi, daga bisani jami'an sun iya gano gawarwakin wadanda suka mutu da kuma wasu wadanda suka tsira da rayukansu.
Masu fasakwabrin jama'a, sun jima suna amfani da kananan kwale-kwale makamancin wanda ya yi wannan hadarin, don shigar da bakin haure Britaniya ta barauniyar hanya, duk kuwa da kwararan matakan da gwamnatin kasar ke dauka na kare iyakarta daga bakin da ke jefa rayuwarsu a cikin hadari da zummar neman mafaka a Britaniyan.