1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkirta shirin Brexit bisa sharadi

Yusuf Bala Nayaya
March 21, 2019

Kudirin da Kungiyar EU ta cimma bisa sharadi ya zo bayan da shugabannin kasashe 27 na kungiyar suka duba batun a ranar Alhamis.

https://p.dw.com/p/3FSUT
EU-Gipfel Brexit Brüssel
Hoto: AFP/Getty Images/J. Thys

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da karin lokaci ga Birtaniya ta karkare da shirin fita daga kungiyar har zuwa ranar 22 ga watan Mayu, idan 'yan majalisar dokokin kasar sun amince da yarjejeniyar da suka cimma da Firaminista May cikin mako guda. Kudirin da Kungiyar ta EU ta cimma ya nunar da haka bayan da shugabannin kasashe 27 na kungiyar suka duba batun a wannan Alhamis.

Kudirin da kamfanin dillancin labaran Reuters ya gani ya nunar da cewa May na da kalubale na gamsar da 'yan majalisa kan abin da ta cimma da EU kafin kara samun lokaci kasancewar a yarjejeniyarsu ta baya Birtaniya na da nan da ranar 29 ga wannan wata ne ta kammala da shirin fita daga EU.