Brexit: May ta gargadi jami′an gwamnati | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Brexit: May ta gargadi jami'an gwamnati

Firaministar Birtaniya Theresa May ta gargadi manyan jami'an gwamnatin kasar ga bukatar sirrinta tattaunawar da aka yi dangane da ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai ta EU.

Gargadin na Mrs Theresa May dai na zuwa ne bayan fahimtar sanar da 'yan jaridu wasu daga cikin batutuwan da aka tabo yayin fara gundarin tattauna a zaman da aka yi a Brussels na kasar Belgium a wannan Litinin.

Ana dai kallon ikon firaministar ta Birtaniya kan jiga-jigan gwamnatin kasar ya sami nakasu musamman kan batun ficewar daga kungiyar ta EU, ganin yadda ra'ayoyin kusoshin gwamnatin suka bambanta kan batun.

Hakan kuwa bai rasa nasaba da sakamakon zaben majalisar kasa da jam'iyyar Mrs. May ta rasa rinjaye ba, wanda ya bude wani sabon babi kan batun ficewar kasar daga EU.