Brexit: EU ta ce bakin alkalami ya bushe
February 7, 2019Talla
Shugagaban hukumar tarayyar Turai Jean Claude Yuncker ya shaidawa Firaministar Birtaniya Theresa May cewa kungiyar EU ba za ta bude wata sabuwar tattaunawa da Birtaniya kan yarjejeniyar Brexit ta ficewar Birtaniya daga kungiyar EU ba.
Sai dai yace suna iya duba yiwuwar yin wasu 'yan gyare gyare kan yarjejeniyar da suka cimma a baya.
Juncker yace kasashe 27 na kungiyar tarayyar Turan suna nan akan matsaya guda game da yarjejeniyar da suka cimma da Birtaniya.
A sanarwar da ya fitar bayan ganawarsa da Theresa May a wannan Alhamis din a birnin Brussels Jean Claude Juncker yace dukkan wata matsaya da za a cimma wajibi ne sai ta sami amincewar majalisar dokokin Turai da kuma daukacin kasashen 27 na tarayyar Turai.