1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Lula ya mika wuya ga 'yan sanda

Gazali Abdou Tasawa
April 8, 2018

Tsohon shugaban Brazil Lui Inacio Lula da Silva ya share darensa na farko a gidan wakafi na ofishin 'yan sanda na birnin Curitiba inda zai yi zaman kason shekaru 12.

https://p.dw.com/p/2vfYL
Brasilien Lula da Silva, ehemaliger Präsident
Hoto: Reuters/L. Benassatto

Tsohon shugaban kasar Brazil Lui Inacio Lula da Silva ya share daransa na farko a gidan wakafi na ofishin 'yan sanda na birnin Curitiba da ke a Kudancin kasar inda zai yi zaman kason shekaru 12 da kotu ta yanke masa bayan da ta same shi da laifin karbar rashawa. 

Tsohon shugaban kasar ta Brazil da ke neman tsayawa takara a zaben shugaban kasa na watan Oktoba mai zuwa, ya isa ne a yammacin jiya Asabar a ofishin 'yan sandan na birnin Curitiba a cikin jirgi mai saukar angulu inda daruruwan masu adawa da shi suka yi ta sowa ta nuna farin ciki da kamun nasa. Sai da ta kai 'yan sanda ga yin amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa magoya bayan tsohon shugaban wadanda suka taru a gaban harabar cibiyar 'yan sandan ta birnin na Curitiba a lokacin zuwan gwanin nasu. 

Da farko dai tsohon shugaban kasar ta Brazil mai shekaru 72 ya bijirewa umurnin kotu na mika kansa ga 'yan sanda a jiya inda ya buya a cibiyar kwadago ta birnin Sao Polo inda dubunnan magoya bayansa suka taru domin kawo masa goyon baya da kuma neman hana a kama shi amma daga bisani ya ba da kai bori ya hau.