1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amazon: Bankin Amirka zai taimaka

Zulaiha Abubakar
September 7, 2019

Shugaba Jair Bolsonaro na kasar Brazil ya gargadi kasashen kudancin Amirka game da yunkurin mika alhakin kare dajin Amazon ga kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3PCln
Kolumbien, Leticia: Amazonas-Länder beraten über Umwelt- und Entwicklungspolitik
Taron gaggawa na shugabannin kasashen yakin Kudancin AmirkaHoto: picture-alliance/AP/F. Vergara

Shugaba Jair Bolsonaro na Brazil din, yayi wannan gargadin ne a lokacin wata hira da ya yi, da kuma aka watsa kai tsaye daga fadar mulkin kasar. A hannu guda kuma, yayin wani taro da shugabannin kasashen kudancin Amirka suka gudanar, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo agajin gaggawa da kuma sanya ido tsakaninsu a lokutan ibtila'i.

A nasa bangaren mai masaukin baki shugaba Ivan Dupue na kasar ta Kwalambiya ya bayyana cewar kasashen bakwai sun bukaci taimakon kudi daga babban bankin kasar Amirka. Wakilai daga kasar Brazil sun hada da ministan harkokin kasashen ketare Ernesto Araujo wanda ya bayyana takaici game da yadda kasashen ketare suka raina kokarin da gwamnatin Brazil ke yi don kare dajin na Amazon. Rahotanni dai sun bayyana cewar tashin gobara a dajin ya ninku da kashi 75 a bana.