Brazil: Binciken cin hanci kan tsohon shugaba Lula da Silva | Labarai | DW | 11.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Brazil: Binciken cin hanci kan tsohon shugaba Lula da Silva

Tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, na fuskantar tuhuma daga alkalin yaki da cin hanci na birnin Curitiba da ke kudancin kasar, inda tsawon awowi biyar ana yi masa tambayoyi.

Brailien Luiz Inacio Lula da Silva (Reuters/P. Withaker)

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva bayan da kotu ta saurare shi.

Sai dai tsohon shugaban mai shekaru 71 da haihuwa, bayan ya amsa tambayoyin ya fuskanci dumbun magoya bayanshi, inda ya yi watsi da zargin da ake yi masa:

"Ban taba neman a bani ba, kuma ban tama karbar wani gida ba kaman yadda ake zargina da shi, na zo gaban kotu ne don yin biyayya ga dokokin da kundin tsarin mulkinmu ya tanada, amma kuma ina mai yi wa wannan shari'a kallon wata manakisa."

Sai nan da zuwa 'yan makonni ne za a iya sanin makomar tsohon shugaban kasar ta Brazil dangane da wannan shari'a, inda ake zargin ya karbi toshiyar baki daga wani kanfanin gine-gine da ake zargin ya bai wa tshon shugaban wani gida a matsayin cin hanci a lokacin yana shugabancin kasar ta Brazil, wanda idan har aka same shi da laifi, to hakan zai dusashe burin da yake da shi na sake dawowa kan karagar mulkin kasar.