Brahimi na cigaba da ziyara a Siriya | Labarai | DW | 24.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Brahimi na cigaba da ziyara a Siriya

Babban mai shiga tsakani a kan rikicin Siriya Lakhdar Brahimi ya isa Siriya a jiya Lahadi domin cigaba da tattaunawa tsakanin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da 'yan tawaye.

++++ Alternativer Ausschnitt +++ epa03398423 A handout photo made available by Syria's Arab News Agency SANA shows Syrian President Bashar Assad (C-R) meeting with the U.N.-Arab League envoy, Lakhdar Brahimi (C-L), in Damascus, Syria on 15 September 2012 for talks that focused on the 18-month-old crisis in the country. Brahimi_s meeting with Assad is the first since he has replaced the former UN Secretary General Kofi Annan. Brahimi, who is on a three-day visit to Syria, held a series of meetings in Damascus with Syrian officials and opposition leaders in order to shape a clear perspective for his future initiative to end the crisis. EPA/SANA / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++

Treffen zwischen Bashar Assad und Lakhdar Brahimi

A wannan Litinin din ce ake sa ran Brahimi da Assad za su yi musayar yawu dangane da halin da Siriyan ke ciki daga bisani kuma ya zanta da bangaren 'yan adawa wanda ke rajin ganin Assad ya kau daga karagar mulki.

Wannan ziyara ta Brahimi dai na zuwa ne daidai lokacin da 'yan tawaye ke zargin jirgin yakin soji ya afkawa wasu mutane da ke kan layin burodi a lardin Hama, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane sittin, baya ga wasu kimanin hamsin da su ka jikkata.

Kisan da aka yi na ranar Lahadi dai shi ne mafi muni ta hanyar amfani da jirgin yaki tun bayan da aka fara rikicin kasar watanni ashirin da dayan da su ka gabata.

Rikicin na Siriya dai ya yi sanadiyyar hallaka mutanen kasar da yawansu ya kai dubu arba'in da hudu, baya ga wasu dubban daruruwa da ya raba da matsugunansu wanda yanzu haka ke gudun hijira a kasashen da ke makotaka da kasar.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasir Awal