1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin kunar bakin a Maiduguri

Abdul-raheem Hassan
June 17, 2018

Akalla mutane 31 sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a tagwayen hare-haren kunar bakin wake a garin Damboa na Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2zj3E
Boko Haram
Hoto: Java

Majiyoyin tsaro a birnin Maiduguri sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa, dan kunar bakin wake ne ya tarwatsa kansa loakcin da al'ummar musulmi ke dawowa daga shagulgulan bikin Salla a daren ranar Asabar.

Hari na biyu kuma ya biyo baya mintoci kalilan bayan da maharan suka harba abun fashewa a taron jama'a da suka kawo dauki kan mutane da harin farko ya ritsa da su. Babu kungiyar da ta dau alhakin harin nan take, amma hukumomi na zargin kungiyar Boko Haram da kai harin.

Wannan harin shi ne mafi muni a baya-bayannan bayan harin kunar bakin wake a kasuwa da kuma masallaci ya kashe mutane 86 a garin Mubi na jihar Adamawa. Kungiyar Boko Haram ta jima tana ta'asa kan fararen hula a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya da wasu jihohin arewacin kasar, abinda ya yi sanadiyyar raba dubban mutane da gidajensu.