Borno: Ta′azzarar hare-haren Boko Haram | Siyasa | DW | 11.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Borno: Ta'azzarar hare-haren Boko Haram

Gwamnatin Borno ta dora alhakin dawowar hare-haren Boko Haram a gabar tafkin Chadi kan sabbin dabaru na maye gurbin kananan sansanonin sojojin Najeriya da manyan sansanonin yankuna

Kusan a iya cewa lamuran tsaro sun dagule a a wannan lokaci inda mayakan Boko Haram ke yin yadda su ka dama yayinda su ka kai hare-hare a sassan bakin gabar tafkin Chadi.

Masana tsaro na kamanta yayain da ake ciki yanzu da shekarun 2013 zuwa 2015 inda mayakan Boko Haram kai kai hare tare da fada wararen da su ke iko da su duk da cewa gwamnati da jami'an tsaro na ikirarin murkushe su.

Hukumomi a jihar Borno da masana tsaro har da ma wasu dattawan jihar da talakawa na gagin hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai na da nasaba da rashin Sojoji a yankunan da dama abinda ya ke baiwa mayakan Boko haram dama kara mamaye wasu yankunan.

Alh Hassan Zanna Buguma daya daga cikin dattawan jihar Borno ne da ya ke ganin sabbin dabarun sun bude hanyoyin na karfafa ayyukan mayakan Boko Haram a bakin gabar tafkin Chadi.

Shi kuma Mustapha Bukar Dambowa wanda aka fi sani da Justice wani mai fashin bakin baki kan harkokin tsaro ya kamata Sojojin su sake dabaru ko da ma za'a hade kanannan sansanonin Sojojin zuwa manya sansanonin.

Sauti da bidiyo akan labarin