1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Birtaniya ya shiga gararin siyasa

Suleiman Babayo AMA(SBA)
July 6, 2022

Ana kara shiga rashin tabbas a fagen siyasar Birtaniya sakamakon murabus da wasu ministocin gwamnati suka yi, inda Firaminista ke kara shiga tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/4DkdF
UK Fragen für den Premierministers | Boris Johnson
Hoto: AFP

Firaministan Boris Johnson na Birtaniya yana kara shiga mawuyacin halin siyasa yayin da masu zuba jari ke saka ido kan mutumin da aka nada a matsayin sabon ministan kudin kasar, bayan murabus din da wasu minisotoci suka yi. Tuni kudin kasar na Fam ya rasa daraja da aka dade ba a gani ba cikin shekaru biyu, idan aka kwatanta da dalar Amirka. Duk da yake ya ji takaicin abinda ya faru, dan majalisar dokokin Birtaniya Peter Bone yace ya ji dadin yadda aka nada sabon ministan kudi.

Karin Bayani: Birtaniya: Iza bakin haure zuwa Ruwanda

"Ministanci biyu sun tafi. Ina tsammani akwai 'yan majalisa 130 da ke cikin gwamnati da hudu suka ajiye aiki, wannan mai yuwuwa ba babban lamari ba ne. Mun samu sabon ministan kudi. Kuma akwai maganar zabtare haraji, abin da ya samo asali tun lokacin tsohon ministan. Na yi murna da sauyin, amma ba na jin dadin abin da ke faruwa."

'Yan majalisar dokokin jam'iyya mai mulki na son gwamnatin ta zabtare haraji.

UK Kabinettssitzung der Regierung | Nadhim Zahawi
Hoto: Christine Ongsiek/Avalon/Photoshot/picture alliance

Shi dai sabon ministan kudin Birtaniya Nadhim Zahawi, an nada shi ne samakon murabus da Rishi Sunak kan mukamun na ministan kudi sannan Sajid Javid ya ajiye mukamunsa na ministan lafiya. Kana a wannan Laraba ita karamar minista Jo Churchill, cikin gwamnatin ta yi murabus, lamarin da ke kara nuna rashin tabbas da gwamnatin Conservative karkashin Firaminista Boris Johnson ke kara shiga. Duk da abin da ke faruwa Peter Bone ya nuna fata kan rashin samun ci gba da masu ajiye mumamai cikin gwamnatin:

"Ba na tsammanin samun ci gaba da ganin masu ajiye aiki, ganin abin da ke faruwa a majalisa. Amma ina tunanin firamnista ya karfafa mambobinsa, idan aka katse samun masu murabus, ina tsammani za mu samu ci-gaba."

Karin Bayani: Birtaniya: Oliver Dowden ya yi murabus

A yayin da dan majalisar ke wannan kalaman ana kara samun baraka da rahotannin masu janye goyon baya ga gwamnatin Conservative karkashin Firaminista Boris Johnson. Wannan murabus da aka samu ya biyo bayan hakruri da Firaminista Boris Johnson na Birtaniya ya bayar kan wasu abubuwa da suka faru na lalata.

Firaministan na amsa tambayoyin 'yan majalisar dokokin kasar sakamakon wannan muramus da aka samu a cikin gwamnatin kasar ta Birtaniya. Keir Starmer shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Labour ke jagoranci tambayoyin da ake yi wa firaministan a gaban majalisar dokokin.