Boren Yahudawan Habasha a Isra′ila | Siyasa | DW | 05.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Boren Yahudawan Habasha a Isra'ila

Banbancin da ake nuna wa Yahudawa 'yan asalin Habasha mazauna kasar Isra'ila abu ne da ya dade, duk da shekarun da aka yi Habashawan na zaune a kasar

Baiyanar faifan bidiyo da ke nuna 'yan sandan Isra'ila na dukan wani dan asalin Habasha da yanzu ke aikin soja a Israela a kasar dai ya sa hukumomi daukar mataki.

Matashi Damas Pakada yana aikin soja ne garin Holon Kudu da birnin Tel Aviv lokacin da ya fito sanye da kakakin soja, sai aka ga wasu 'yan sandan Isra'ila sun danne shi suna cin zalinsa, duk kuwa da shi sojan kasar ne, amma kasancewa shi bakar fata bai sa ya tsira ba.

Sai dai fitar faifan bidiyo a bainar jama'a ta kai gwamnatin Isra'ila ta sallami 'yan sandan, a woni mataki da ke nuna mai yiwa an fara samar wa Habashawan 'yanci. Fetahun Assefa-Dawit babban darakta ne a kungiyar kare 'yancin 'yan asalin Habasha a Isra'ila.

"Muna da karin maganar cewa bulalar da ta karya tuson ragumi, shi ne abin da ya faru ranar Lahdin da ta gabata, inda sojan rundunar tsaron Isra'il da ke da asalin kasar Habasha ya sha duka a hannun 'yan sanda biyu, ba tare da aikata wani laifi ba. Kuma kusan dukkan mutane da kake ganin a nan kowa ya taba dandana wannan muzgunawar yan sanda".

Hakika 'yan asalin Habasha da ke Isra'ila na ganin tura ta kai bango, don haka ma dubbansu suka fito yin bore kan titi a ranar Lahadi bayan faruwar lamarin, inda suke Allaha wadai da wariyar da ake nuna musu, musamman a hannun 'yan sandan Isra'ila. Dr Gadi Ben Ezer farfesa a jami'an Ben Gurion, kuma yana cikin wadanda suka shiga zanga zangar a Tel Aviv.

"Nuna babbanci wa yan Habasha na faruwa a ko wani fanni, kuma dole a kawo karshensa, badon yan asalin Habasha ba, amma don mu kanmu. Don mutuncinmu ba nasu ba".

A zanga-zangar da aka yi dai mutane da dama suka jikkata, ciki harda 'yan sanda 55 da kuma fararen hula 12. An kuma tsare mutane da yawa. Firaminista Benjamin Netanyu ya fada wa 'yan kasar cewa, duk wani muzgunawar 'yan sanda ana gudanar da bincike, amma kuma kuma tarzoma ba abu ne da za'a lamunta ba.

A cewar kungiyar kula da hakkin Hashawan Isra'iladai, kimanin kashi 49 na Habasha Yahudawa, na rayuwa cikin talauci da rashin Ilimi, ga kuma rashin mahalli, abin da ke barazanar kawo wani babban tashin hankali, in aka kwatanta da Yahudwan Isra'ila dake rayuwa mai inganci.

Sauti da bidiyo akan labarin