Boren neman murabus din shugaban Mexiko | Labarai | DW | 16.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren neman murabus din shugaban Mexiko

'Yan kasar Mexiko sun yi zanga-zangar bukatar shugaban kasar Enrique Pena Nieto ya yi sauka da mulki bisa zargin gwamnatinsa da rashawa.

Dubun dubatan masu zanga-zangar dauke kwalaye da aka rubuta cewar " Tilas ya sauka" " Ba ma so" Masu gangamin dai sun fito ne daga daukacin jihohin kasar, da zimmar nuna kyamar salon shugabancin shugaba Enrique Pena Nieto.

A wani kira ta kafar sada zumunta da ya yi tasiri wajen hada kan iyayen dalibai 43 da 'yan sanda suka yi garkuwa da su sama da shekaru biyu, tare da wasu 'yan kasar ta Mexiko sun amsa kiran yin tattaki izuwa masaukin shugaban kasar. Inda suke alakanta mulkin shugabansa da wanda ke cike da kazamin cin hanci da rashawa da ya rufe masa idanu wajen warware matsalolin da kasar ke fama da su tun kama mulkinsa.

Enrique Pena Nieto mai shekaru 50 da haifuwa wanda ya shafe shekaru biyar a kan mulki, yana fuskantar suka daga 'yan kasar a kan yadda yake sakaci da harkar safarar muggan kwayoyi. To sai dai ganawarsa da dan takaran shugabancin Amirka Donald Trump, na cikin abinda ya hargitsa 'yan kasar neman tilastawa ya yi murabus.