Bore kan sansanin sojin Amirka a Japan | Labarai | DW | 19.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bore kan sansanin sojin Amirka a Japan

Dubban mutane sun yi da zanga-zanga mafi girma da aka taba a 'yan shekarun nan a tsibirin Okinawa da ke kasar Japan inda Amirka ke da sansanin sojojinta.

Wannan zanga-zanga ta biyo bayan kisan wata mata 'yar Japan da aka yi wadda ake zargin wani dan Amirka da yin kisan a wannan tsibiri wanda ke dauke Amirkawa kimanin dubu 50 wanda dubu 30 daga cikinsu sojoji.

Yanayin da yanzu haka aka shiga ya nuna irin alkiblar da dangantaka tsakanin firaministan Japan Shinzo Abe da shugaban Amirka Barack Obama ta dosa, inda masu sanya idanu kan lamarin ke cewar batun na kokarin jefa bangarorin biyu cikin takun saka. Halin da ake ciki dai ya sanya hukumomin Japan din yin barazanar dauke sansanin sojin Amirkan daga tsibirin na Okinawa zuwa wani waje na daban da ke da karancin jama'a.