Bore kan babbancin jinsi a Amirka | Siyasa | DW | 25.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bore kan babbancin jinsi a Amirka

Har yanzu tsugune bata kare ba kan boren da bakaken fatar Amirka ke yi, bisa matakan 'yan sanda a Ferguson bayan da kotu sallami wanin dan sanda da yarbi wani bakar fata.

Jami'an 'yan sanda a Amirka na cikin wani yanayi na tsaka mai wuya, ba wai kawai don kisan matashin Micheal Brown dan shekaru 18 bakar fata a Ferguson na yankin Missouri kawai ba, amma biyo cewa alkalan da suka jagoranci zaman nazarin shaidun da aka gabatar kan kisan da dan sanda Darren Wilson ya yi wa matashin inda alkalan suka ce, dan sandan ya yi kisan ne a kokarin kare kai, lamarin da yanzu ya tada mummunar zanga-zanga da ta biyo bayan sakamakon shari'ar.

Bob McCulloch, da ke zama a bangaren mai gabatar da kara, ya ce hukuncin dai ya biyo bayan shaidun da alkalan da suka yi nazari a kansu.

"Sun amince kuma sun kammala wannan hakki da ya rataya a kansu, bisa adalci da bin matakai da doka ta tanada. Abu da ke da muhimmanci anan shi ne a gane cewa su mutane ne, da ke duba ko wace shaida da aka gabatar musu, su yi nazarinta. Sun tattauna sun kuma sun yi muhawara kan irin shaidun da aka gabatar musu, kafin su fitar da wannan hukunci na bai daya, bayan kammala bincikar shaidun da aka gabatar musu, masu gudanar da irin wannan bincike kan miyagun laifuka a kotu bayan kwanaki biyu na nazari sun fitar da sakamakonsu na karshe".

Fitar sakamakon dai ya sanya shugabannin jan hankulan masu zanga-zangar, kada su dau doka a hannunsu a mutunta doka, kamar yadda shugaban na Amirka Barrack Obama ke cewa.

"Abu na farko shi ne wannan kasa ce da ke bin doka da oda, ya kamata mu lura mu karbi wannan hukunci da jagoran alkalan da suka binciki shari'ar ya fitar. Akwai Amirkawa da suka yi lale marhabun da hukuncin, akwai kuma wadanda basu yi ba, har ma hukuncin ya bakanta musu rai. Abu ne da za a iya fahimta, amma na ina tare da mamhaifan Micheal Brown, cewa duk wanda ya shiga wannan zanga-zanga ya yi ta cikin kwanciyar hankali".

Wannan zanga-zanga dai da shugaba Obama ya bukaci ganin ta zama ta lumana, akasin haka ke wakana a yankin na Furgusson, inda taron dubban matasan da suka tattaru a Furguson a daren jiya Litinin, suka afkawa shaguna da sace-sace da ma banka wuta ga gine-gine da motoci, ciki harda na 'yan sanda. Kamar yadda Jon Belmar, shugaban 'yan sanda a ofishin St. Louis ke cewa.

Ya ce "Na sani akwai gine-gine da-dama da aka sanyawa wuta, aksarinsu sun kone kurmus. Na san cewa akwai wasu motocin 'yan sanda na yankin St.Louis da aka kone, akwai 'yan sanda da dama da suka sha ruwan duwatsu dama duk abinda ya zo hannun masu zanga-zangar, ni da kaina na ji karar bindiga da aka harba kamar sau 150".

Amfani da karfin jami'an tsaro da ya wuce kima dai, na zama babban kalubale ga 'yan sandan yanki a kokarin kwantar da wannan tarzoma da ke ci gaba da gawurta.

Sauti da bidiyo akan labarin